
Za a samu Miliniyoyi 60 a dalilin tsarin garabasar Kamfanin simintin Dangote
A wannan zango na tsarin garabasar kamfanin Dangote, ana neman samar da masu kudi 60 a jihohin kasar nan, kamfanin ya na wannan ne domin rage radadin COVID-19. Annobar cutar COVID-19 da ta addabi ta karya tattalin arzikin mutane da kasashe,
wannan ya sa kamfanin Dangote Cement ya sake kawo wannan tsari a Najeriya. Shugabar harkar kasuwanci da kamfanin, Misis Funmi Sanni, ta shaida cewa duk da mutanen su ka yi dace, akwai karin wadanda za su samu gawurtattun kyaututtuka.
A wajen gabatar da kyatuttuka ga wadanda su ka yi nasara, Funmi Sanni ta ce mutane 27 sun taki babbar sa'a, kuma kudinsu sun shigo masu a makon da ya gabata.
A cewar darektar, masu ciniki a kamfanin Dangote za su iya samun kyauta har ta Naira miliyan daya bayan sun karbi wasu kati da ke dauke da wasu jerin harufa. Duk wanda ya yi dacen cinko harufan D, A, N, G, O, T da E, ya hada sunan DANGOTE, zai tashi da wasu daga cikin jeringiyar kyaututtukan da ake rabawa a Birane.
Rahoton ya ce irin kyaututtukan da ake samu daga kamfanin simintin na Dangote sun hada da babur, keke napep, akwatin talabijin, katin wayar salula da dai sauransu. Za a rufe wannan garabasa ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2020 inji kamfanin.
Wani babban jami’in kamfanin Dangote, Rabiu Umar, ya ce sun kawo wannan shiri ne domin agazawa mutane a sakamakon annobar COVID-19 da ta rutsa da Bayin Allah.
Umar ya ce kamfanin Dangote zai rabawa mutum 1000 kyautar Naira Biliyan daya. Ya ce: “Mu na ganin cewa duk da annobar nan, ya kamata mu sa masu ciniki da mu farin ciki.”
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Za a samu Miliniyoyi 60 a dalilin tsarin garabasar Kamfanin simintin Dangote "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?