
Za a jefe tsoho dan shekara 70 mai fyade a Kano
Kotun, mai zamanta a Kofar Kudu ta yanke wa tsohon Mati Audu hukuncin ne a zamanta na ranar Laraba.
Alkalin kotun, Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya yanke hukuncin ne bayan da tsohon dan asalin yankin Falsa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa a Jihar ya amsa laifin da kansa.
Tun da farko dai an zargi tsohon ne da yi wa wata yarinya mai kimanin shekaru 12 fyade, laifin da ya yi ikirarin aikatawa a zama daban-daban har karo uku.
Alkalin ya ce hukuncin ya yi daidai da tsarin Shari’ar Musulunci da ya tanadi hukuncin rajamu kan duk wanda aka samu da aikata zina matukar dai ya taba yin aure.
Hukuncin na zuwa ne kwana biyu bayan wata kotun Shari’ar Muslunci ta yanke wa wani matashi mai suna Yahaya Sharif Aminu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin batanci ga Ma’aiki (SAW).
SOURCE: AMINIYA DILY TRUST
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Za a jefe tsoho dan shekara 70 mai fyade a Kano"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?