Yadda aka kama babban jami'in gwamnati yana lalata da sakatariyarshi a ofis a lokacin da yake ganawa da abokanan aikinshi a kiran bidiyo na zoom
Friday, 28 August 2020
Comment
Asirin wani babban ma'aikacin gwamnati a kasar Philippine ya tonu, bayan an kama shi yana lalata da sakatariyar shi
Mutumin dai ya fara taron kiran bidiyo a manhajar Zoom ke da wuya sai ya koma yana lalata da sakatariyar tashi bai san cewa kowa na gani ba - Bayan sun kammala ya dawo ya cigaba da ganawa da abokanan aikinshi kamar babu abinda ya faru
An kama wani babban jami'in gwamnati yana lalata da sakatariyarshi a cikin ofis a lokacin da rashin sani ya sanya ya fara kiran waya na bidiyo da abokanan aikin shi a kasar Philippines.
Kamar yadda rahoto ya nuna, ma'aikata daga garin Fatima Dos dake Cavite suna gabatar da taro ta manhajar zoom kamar yadda suka saba a ranar Laraba.
Shugabansu Jesus Estil, wanda aka bayyana cewa bashi da ilimi akan harkokin na'ura mai kwakwalwa yaje ya danna wani wuri sai kyamarar na'urarshi ta fara aiki.
Bayan sun fara taron, shugaban nasu ya tashi daga kan kujerarshi ya tinkari wata mata dake zaune a can gefe, bayan dakiku kadan, kawai sai gani aka yi sun fara lalata yayin da sauran abokanan aikinshi suke kallo. Daga baya shugaban da matar sun dawo sun cigaba da halartar taron basu san cewa asirinsu ya tonu ba.
Daga baya an gano cewa wannan matar ashe sakatariyar shi ce, wacce kuma ita ce ke kula da harkar kudi a ofishinsa. Bidiyon wanda daya daga cikin ma'aikatan ya dauka, an wallafa shi a shafukan sadarwa, inda hakan ya jawo mutanen garin suka bukaci a cire mutumin daga mukaminsa. Ma'aikatar cikin gida da kananan hukumomi ta tabbatar da cewa za a kori Estil daga kan mukaminsa cikin gaggawa.
Shugaban ma'aikatar Cif Richard Geronimo, ya ce: "Wannan ba karamin laifi bane, babban laifi ne. Zamu yi iya bakin kokarinmu wajen hukunta shi." Estil dai ya bukaci a yafe masa, amma ina hakan bai yiwu ba.
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yadda aka kama babban jami'in gwamnati yana lalata da sakatariyarshi a ofis a lokacin da yake ganawa da abokanan aikinshi a kiran bidiyo na zoom "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?