
Wani mutum ya kai hari fadar White House, ya tilastawa Trump guduwa daga dakin taro
Tuesday, 11 August 2020
Comment
dogaran Trump suka garzaya wajensa yayinda yake jawabi kan mumbari kuma sukayi gaba da shi. Dogarin ya ce masa, "Yallabai biyo ni mu tafi." Ba tare da bata lokaci ba, Trump da mukarrabansa suka wuce kuma aka garkame kofar dakin taron cike da yan jarida.
A wajen fadar, an ga jami'an tsaro suna guje-guje suna boyewa bayan bishiyoyi. A cewar Fox News, wadanda kamarorinsu ke waje, an ji harbe-harbe har sau biyu.
Daga baya Trump ya dawo dakin taron inda yayi bayanin cewa an bindige maharin kuma an garzaya da shi asibiti.
Trump ya ce lokacin da jami'an tsaro suka fita da shi, ofishin Oval suka kaishi . "Harbi aka ji a wajen fadar White House. Amma komai yayi daidadi yanzu... Amma anyi harbe-harbe kuma an garzaya da wani asibtii. Ban san halin da yake ciki ba."
Trump yace. Daga bayan hukumar tsaron fadar White House, ta saki jawabin cewa "daidai misalin karfe 5:53 na yamma wani mahari ya kaiwa jami'in tsaro dake gadin fadar hari kuma ya ciro wani abu daga aljihunsa.
"Ganin kaman cewa ya ciro makamai, hakan ya sa jami'in tsaro ya bindigeshi." Jawabin hukumar yace. An garzaya da mutumin da jami'in tsaron asibiti kuma za'a binciki lamarin, hukumar ta kara.
SOURCE LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Wani mutum ya kai hari fadar White House, ya tilastawa Trump guduwa daga dakin taro "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?