
Uba da Amaryarsa sun kashe diyar uwargida don tayi fitsari a wando
kasar Amurka bayan kisan diyar uwarigida mai shekaru takwas da haihuwa, Autumn, bayan daureta cikin jakar leda don ta yi fitsari a wando. An tsinci gawan yarinyar cikin randan wanka misalin karfe 3:45 na rana yayinda aka kira jami'an yan sanda, Daily Mail ta ruwaito.
A cewar ofishin yan sandan Sherburne County, yayinda suka dira wajen sun samu kishiyar mahaifiyar yarinyar, Sarah Hallow, tana kokarin farfado da yarinyar.
Duk yunkurin da aka yi na ceton rayuwarta ya ci tura yayinda aka sanar da mutuwarta a lokacin. Masu bincike sun bayyana cewa da yiwuwan ta dade da mutuwa kafin a kira yan sanda,
saboda yanayin yadda aka samu jikinta. Tuni an garkame Uban yarinyar, Brett Hallow da amaryarsa, Sarah Hallow kuma an tuhumesu da laifin kisan kai, a cewar Twin Cities Pioneer Press.
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Uba da Amaryarsa sun kashe diyar uwargida don tayi fitsari a wando "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?