
Tubabbun ɗan bindiga ya fada mana daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya - Mailafia
Tuesday, 11 August 2020
Comment
Mailafia ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Nigeria Info FM a ranar 8 ga watan Agustan shekarar 2O2O.
Kalamansa; "Bari inyi bayyana wasu abubuwa domin wasu daga cikin mu muna binciken sirri mu ma. Mun gana da wasu daga cikin yan bindiga da suka tuba, daya ko biyu daga cikinsu. Mun tattauna ba sau daya ba ba biyu ba.
"Sun fada mana cewa daya daga cikin gwamnonin jihohin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya. "Boko Haram da yan bindiga duk daya ne a Najeriya. Suna da tsari mai sarkakiya da wuyan gane wa. "
A lokacin kullen korona, jiragen su na ta zirga zirga suna kai makamakai da kudade zuwa sassa daban daban a kasar kamar babu dokar kulle.
"Sun riga sun isa kudu. Babu inda babu su. Sun ce mana idan sun gama kai hare hare kauyuka, za su shiga mataki na biyu. Mataki na biyu shine za su fara kai hari birane suna zuwa gidan manyan mutane suna kashe su. Ina tabbatar maka, wannan shine tsarin su.
"Zuwa shekarar 2022, suna son su fara yakin basasa a Najeriya. Kada ku dauka abinda na ke fadi wasa ne. Na yi digiri na ta 3 a Jamiar Oxford. Ni kuma kwararren maaikacin banki ne. Ba mu fadin shashanci. "Kada kayi wasa da abinda na ke fada maka."
Da aka tambaye shi ko gwamnan da ya ambata da farko, tsohon gwamna ne ko mai ci yanzu, Obadiah ya ce. "Yana kan mulki yanzu. Ya ce daya daga cikin gwamnonin ne kwamandan Boko Haram a Najeriya kuma ba kudi suke nema ba, suna da isassun kudi."
Ga dai bidiyon hirar nan a kasa;
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Tubabbun ɗan bindiga ya fada mana daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya - Mailafia"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?