
Tsohon gwamna a Najeriya ya yi kaca-kaca da karuwarsa, 'yan sanda sun damkesu
Budurwar na zama a jihar Legas inda take kasuwancin kayan sawa. Ana zargin cewa alakarsu ta baci ne bayan da Amuchienwa ta yi kokarin bata masa suna, lamarin da yasa ya kira mata 'yan sanda. Budurwar ta zargi tsohon gwamnan da bata zoben lu'u-lu'u amma na bogi don saka ranar bikinsu.
Ohakim yana da shekaru 63 a duniya kuma yana da mata mai suna Chioma wacce suka kwashe shekaru 39 da yin aure. Suna da 'ya'ya biyar da jikoki.
A wata takardar korafi da tsohon gwamnan ya mika ga sifeta janar na 'yan sandan Najerya, Mohammed Adamu, Ohakim ya ce, "A ranar Asabar, 18 ga watan Janairun 2020, Chinyere ta ci zarafina. "Ta yaudareni inda ta bukaci ganina.
Daga bisani na gayyaceta dakin otal dina da Asokoro a Abuja inda ta iso wurin karfe 8:15 na yamma. "Ina bude kofa ta hau ni da duka har da shako wuyan rigata da dukkan karfinta.
Ban yi sanya ba na tureta." Ohakim ya ci gaba da cewa, "A yayin da nake kokarin tashi, ta yi kokarin kwace wayata amma na karba da karfi. Ta gaggauta daukar jakarta inda na yi zaton bindiga za ta fito da ita."
Ohakim ya ce da gaggawa ya fita yana ihun neman taimako. A cewarsa, za a iya amfani da CCTV ta otal din wurin tabbatar da ikirarinsa. Daga nan ne ya kira jami'an 'yan sanda da ke ofishinsu na Asokoro don kama karuwar ta shi.
Tsohon gwamnan ya tabbatar wa da 'yan sanda cewa Amuchienwa na da shekaru 56 a duniya kuma bazawara ce. Ya ce Amuchienwa ta kasance kawarsa wacce ya ke yi wa alfarmma daban-daban, kuma ta kasance daya daga cikin wadanda suka yi ruwa da tsaki wurin yakin neman zabensa. Amma ya ce,
wannan alakar ta lalace kuma tuni take yunkurin bata masa suna tare da ganin bayansa. Ya ce ya matukar razana kuma yana son shugaban 'yan sandan Najeriya ya shiga lamarin.
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Tsohon gwamna a Najeriya ya yi kaca-kaca da karuwarsa, 'yan sanda sun damkesu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?