
Tserewar mai laifi: Matasa sun yi wa 'yan sanda ruwan duwatsu yayin zanga-zanga
Suna bukatar a tsananta bincike a kan lamarin tare da hukunta duk wani dan sanda da ke da hannu, jaridar Daily Trust ta wallafa. Sakamakon zanga-zangar, an samu cushewar hanyar tsakanin hedkwatar 'yan sandan da kuma tashar motar Eleyele. Ganau ba jiyau ba,
sun sanar da manema labarai cewa masu zanga-zangar sun matukar fusata kuma sun dinga jifan 'yan sandan da duwatsu tare da wasu makamai masu hatsari. Wasu masu zanga-zangar, wadanda da yawa daga ciki dalibai ne na gaba da sakandare, suna dauke da fastoci inda suka yi tattaki har zuwa hedkwatar 'yan sandan da ke yankin Eleyele
A yayin jawabi ga fusatattun matasan, kwamishinan 'yan sandan jihar, Nwachukwu Enwonwu, ya tabbatar da cewa za a damko wanda ake zargin tare da gurfanar da shi. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi,
ya ce wasu daliban sun yi zanga-zangar a babban ofishin 'yan sandan jihar. Fadeyi ya ce: "Kwamishinan 'yan sanda da sauran manyan jami'a sun sauraresu kuma sun amsa musu tambayoyinsu. "Kun san daliban yanzu dai, wasu mun kasa shawo kansu amma mun yi jarumtar shawo kansu sakamakon kwarewarmu. "Tuni sun koma."
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Tserewar mai laifi: Matasa sun yi wa 'yan sanda ruwan duwatsu yayin zanga-zanga "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?