
Tirkashi: Hotunan matar da ta yi shagalin mutuwar aurenta
'Yan kasar Afrika ta Kudun sun matukar girgiza da abinda ya faru inda suka dinga tofa albarkacin bakinsu Wata mata ta ja hankalin jama'a a kafar sada zumuntar zamani bayan da ta yi bikin shagalin murnar mutuwar aurenta. A ranar Litinin, 17 ga watan Augusta, wata ma'abociyar amfani da Twitter mai suna Lungi Shozi, ta wallafa hotunan.
Matar ta siya wa kanta kek inda aka rubuta: "Na yi, na gama, na kammala. Mun rabu daga karshe." Shozi ta yi rubutu kamar haka a kasan hotunan: "A yanzu jama'a har bikin shagalin mutuwar aure ake yi."
'Yan kasar Afrika ta Kudu sun kasa kyale hotunan a haka, amma sai suka bi sashen tsokaci inda suka dinga tofa albarkacin bakinsu. Malusi luso ya yi tsokaci kamar haka:
"Duniya yanzu ta aminta da rashin hankali. Duba, ba shagalin a kan kwanciyar hankali take yi ba, bacci ba tare da kuka ba, rashin dukan miji da sauransu."
Duk da ba wannan bane karo na farko da aka fara shagalin murnar mutuwar aure ba, wani mutum ya bayyana na shi. A kwanakin baya, bawan Allan ya fito inda ya nuna farin cikinsa bayan rasuwar aurensa.
Matashin ya sanar da rabuwarsa da matarsa inda ya ce ya dawo daga kangi. A wasu hotunan mutumin da suka bayyana, an gan shi tsaye a gaban wata babbar mota inda aka rubuta "yanzu mun rabu" ta tagar bayan motar.
A bayyane murnar mutuwar aurenshi ya ke a fuskar matashin kuma hotunan sun ba zu a kafafen sada zumuntar zamani
People celebrate their divorce now😭 pic.twitter.com/T7dXQWyqGu
— Lungi Shozi♒🇿🇦 (@IamlungiDee) August 17, 2020
SOURCE: LEGIT.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Tirkashi: Hotunan matar da ta yi shagalin mutuwar aurenta "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?