
Sheik Zakzaky ya raba magunguna da gidajen sauro a sansanonin 'yan gudun hijira
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi sun godewa Sheik Zakzaky da irin kokarinsa, tare da addu'ar Allah ya sa a sake shi Shugaban mabiya akidar Shi'a, Sheik Ibrahim Zakzaky a ranar Talata ya raba tallafin magunguna da gidajen sauro ga mazauna sansanonin gudun hijira a karamar hukumar Faskari, jihar Katsina.
Wakilin Sheikh Zakzaky a Funtua, Sheik Rabiu Abdullahi ya ce shehin ya zabi sansanin Faskari domin tallafawa mazauna sansanin da suka bar garuruwansu sakamakon hare haren 'yan bindiga.
"Mun ji dadin ganin yadda iyaye mata da kuma wasu rukunin matan da suka zo karbar gidajen sauron da magunguna a cikin sansanin 'yan gudun hijirar," a cewarsa. Ya ce wannan tallafin anyi shi ne domin nuna soyayya da jin kai, tare da nuni da cewa Sheik Zakzaky zai ci gaba da bada tallafi duk da yana a kulle, musamman a wannan yanayi.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saki jagoran nasu domin duba lafiyarsa, yana mai cewa "tun bayan kisan gillar da gwamnati ta yiwa 'yan uwanmu a Zaria muka yi kira ga jama'armu cewa idan an taba mutum daya, kamar dukanmu ne aka taba."
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi sun godewa Sheik Zakzaky da irin kokarinsa, tare da addu'ar Allah ya sa a sake shi.
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Sheik Zakzaky ya raba magunguna da gidajen sauro a sansanonin 'yan gudun hijira "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?