
Rundunar soji ta fara dibar sabbin soji - Yadda za ka shiga
DSSC26/202 sune wadanda zasu shiga aikin a bangaren hukumar soji da suka samu gajeren horo na kai tsaye, yayin da SSC47/2021 zasu shiga a bangaren hukumar soji da suka samu gajeren horo na musamman. Shelkwatar rundunar sojin ta bayyana hakan a shafinta na Twitter, tana mai cewa nan take ne za a fara cike gurbin aikin, kuma kyauta ne.
"Muna sanar da masu sha'awar shiga aikin soji a matakin SSC47/2021 da DSSC26/2021, da su sani mun bude shafin cike gurbin aiki, za a fara nan take," a cewar rundunar sojin.
Ga hanyoyin da zaka bi domin cike gurbin aikin soji a 2020.
Da farko ka shiga shafin daukar aiki na rundunar da ke a yanar gizo recruitment.army.mil.ng ko ka ziyarci babba shafin rundunar sojin kai tsaye. Ka zabi bangaren aikin da kake so.
Ka dora dukkanin takardunka kamar hoto, takardun kammala karatu, takardar haihuwa ko rantsuwar shekaru, takardar asalin jiha, takardar shaidar zama mamban wata cibiya. A yayin kammala rejistar, ana so masu sha'awar aikin su sauke shaidar yin rijistar a takarda.
Ana son wani magatakardar kotun shari'a ya sa hannu a fejin farko na shaidar yin rejistar da aka saukar, yayin da shugaban karamar hukuma zai sa hannu ko wani babban jami'in soji, a matakin Laftanal Kanal, zai sa hannu a feji na biyu na takardar
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Rundunar soji ta fara dibar sabbin soji - Yadda za ka shiga "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?