
Ronald Koeman zai zama sabon Kocin Barcelona, Quique Setien zai yi waje
Josep Bartomeu, Barça president, just confirmed to @tjcope that Quique Setién “has been sacked”. Ronald Koeman, Mauricio Pochettino and Xavi are in the list as next manager. 🔵🔴 #FCB #Barcelona
— Fabrizio Romano (@FabrizioRomano) August 16, 2020
Rahotanni daga jaridun kasashen Turai sun nuna kungiyar Barcelona za ta nada kocin kasar Holland, Ronald Koeman a matsayin sabon kocinta a cikin farkon makon nan. Shararren ‘dan jaridar nan Fabrizio Romano ya ce Barcelona ta na shirin sallamar Quique Setien daga kujerar mai horas da manyan ‘yan kwasan kwallon kafanta.
Hakan na zuwa ne bayan Bayern Munich ta kunyata Barcelona a gasar cin kofin Nahiyar Turai. Bayern ta lallasa kungiyar Sifen din ne da ci 8-2 kwanan nan.
Tsohon kocin Everton, Ronald Koeman ya kwantawa Barcelona a rai, kuma rahotanni sun ce za a tsaida shi a matsayin sabon koci da zarar an yi waje da Quique Setien. Wani kocin da ake hangen zai iya rike Barcelona a wannan lokaci shi ne Mauricio Pochettino wanda kungiyar Tottenham ta sallama a karshen shekarar da ta wuce.
Matsalar da Barcelona za ta samu wajen daukar hayan Mauricio Pochettino shi ne da wuya ya yarda ya yi aiki da kungiyar a matsayinsa na tsohon kocin Espanyol. Tsohon ‘dan wasa Xavi Hernandez wanda ya yi ritaya daga kungiyar 2014 ya na tare da Al-Sadd,
kuma bai da niyyar barin kasar Qatar a daidai wannan lokaci. Hakan ya sa ake ganin Ronald Koeman ya zama sabon kocin Barcelona ya gama. Kocin mai shekaru 57 ya bugawa kungiyar kwallo tsakanin shekarar 1989 zuwa 1998.
Koeman ya kuma yi aiki da Barcelona a matsayin mataimakin koci daga 1998 zuwa 2000. Bayan nan ya rike kungiyoyi irinsu Ajax, Benfica, PSV, Valencia, AZ, da Feynoord. Haka zalika tsakanin 2014 zuwa 2017, Ronald Koeman ya yi aiki a Ingila, ya horas da kungiyoyin Southampton da Everton a gasar Firimiya, daga nan kasarsa ta yi hayarsa.
Ronald Koeman has been choosen as new Barcelona manager. He's going to leave Holland National team to join Barça - official statement on this week. Here we go! 🤝🔵🔴 #FCB #Barcelona #Koeman
— Fabrizio Romano (@FabrizioRomano) August 17, 2020
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Ronald Koeman zai zama sabon Kocin Barcelona, Quique Setien zai yi waje "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?