
Miyagun ‘Yan bindiga sun hallaka ‘Dan Majalisar Baraza/Dass, Hon. Mante Baraza
Jaridar Leadership ta Najeriya, ta fitar da rahoto da safiyar Juma’a, 14 ga watan Agusta, 2020, cewa an hallaka wani ‘dan majalisar jihar Bauchi jiya. Rahoton ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun shiga gidan Hon. Musa Mante Baraza sun kashe shi.
Wannan mumman lamari ya auku ne a daren Juma’a. Kafin mutuwarsa, Musa Mante shi ne mai wakiltar yankin mazabar Dass da Baraza a majalisar dokokin jihar Bauchi da ke Arewa maso gabashin kasar.
Wadannan miyagu da ake zargin cewa ‘yan fashi da makami ne, sun kuma dauke mai dakin marigayin, sun yi gaba da ita, a cewar jaridar.
Daga lokacin da wannan abu ya faru a ranar Alhamis cikin tsakar dare, babu wanda ya ji labarin inda matar ‘dan majalisar ta ke har zuwa yanzu.
A wani rahoton da ya fito daga Wikki Times, ana zargin cewa an sace wasu mutum uku daga cikin iyalin marigayi Musa Mante Baraza. Kafin rasuwarsa, Honarabul Musa Mante Baraza, shi ne shugaban kwamitin sauraron korafi na majalisar dokokin jihar Bauchi.
Bayan haka Mante Baraza ya na cikin kwamitocin tattalin arziki da na harkar noma a majalisar. Kakakin ‘yan sanda na jihar Bauchi, DSP, Ahmed Mohammed Wakili ya tabbatar da wannan kisa, ya ce an sace mata biyu na ‘dan majalisar da ‘dansa. Yanzu haka marigayin ya na kokarin murmurewa ne bayan kwanakin baya ya yi ta fama da cutar COVID-19. Ainihinsa mutumin garin Baraza ne.
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Miyagun ‘Yan bindiga sun hallaka ‘Dan Majalisar Baraza/Dass, Hon. Mante Baraza"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?