--
Mazauna Abuja sun koka a kan yawan sace-sacen mutane

Mazauna Abuja sun koka a kan yawan sace-sacen mutane

 

Wasu yankuna a babbar birnin tarayya na fuskantar yawan garkuwa da mutane

- Mazauna yankunan sun ce a yanzu su kan koma gidajensu kafin karfe 7:00 na yamma saboda ayyukan wasu ‘yan bindiga da ba a sani ba


Sun kuma yi korafin cewa jami’an ‘yan sanda da ke tsaron unguwanni da dama basu isa ba


Wani rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa wasu mazauna yankin Life Camp da ke babbar birnin tarayya, Abuja sun koka kan hauhawan yawan garkuwa da mutane a yankin.


Mafi akasarin mazauna unguwannin Menreng, Winning Clause, Canaan, Dabo Lias, Kingstown da Katsina duk a yanki guda na korafi.


A cewar mazaunan, a yanzu su kan koma gidajensu ne kafin karfe 7:00 na yamma domin tsoron kada ‘yan bindiga su yi gaba da su.


Daya daga cikin shugabannin kungiyar unguwannin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce biyu daga cikin wadanda abun ya cika da su na zama ne a Estate din Katsina.


Ya ce ‘yan bindigan na amfani da damar wani kwana mai zurfi da jeji tsakanin Dabo da unguwan Katsina wajen farma mazauna, sannan su yi ta harbin motocinsu wanda hakan kan tursasa su tsayawa sannan su kuma su sace su.


Ya ce: “Mun samu lamarin guda biyu, daya kimanin wata guda da ya gabata, an yi garkuwa da daya daga cikinmu kuma mun biya fansa kafin all sake shi.


“Yana hanyar zuwa unguwarsa da misalin karfe 11:00 na dare. Ya ga wasu ‘yan bindiga su takwas a wajen sannan suka fara harbinsa, ya tsaya sai suka yi garkuwa da shi.”


Ya ce ofishin yan sanda mafi kusa shine a Life Camp amma ya yi korafin cewa akwai karancinsu a unguwannin


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Mazauna Abuja sun koka a kan yawan sace-sacen mutane"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?