--
Matar da ke auren maza biyu a lokaci guda kuma suke zaune gida ɗaya (Hotuna)

Matar da ke auren maza biyu a lokaci guda kuma suke zaune gida ɗaya (Hotuna)

Sai dai a yanzu zamani ya canja har ta kai ga wasu matan suna auren mazaje biyu ko fiye kuma su zauna da su lafiya a gida ɗaya su haifa musu yara. 

Wata mata mai amfani da dandalin sada zumunta ta wallafa hotunan ta tare da maza biyu da yara da ta ce mazanta ne kuma suna zaune lafiya. Kenya Stevens mace mai maza biyu ta ce har yanzu tana iya tsunduma wa cikin kogin soyayya da wani idan tasu ta zo ɗaya. 



Ta wallafa hotun mazanta biyu, Rakhem Seku, mai bawa mutane shawarwari kan zamantakewar soyayya kuma marubucin littafai. 

Tana kiran su 'Hubby 1' da 'Hubby 2' wato miji na farko da miji na biyu har wasu lokutan ta ke yi musu ba'ar cewa za ta ƙara miji na uku. 

Ta ce sun kwashe shekaru tare da mazan biyu kuma ta haifa musu yara har ma sun girma. Su kan wallafa hotunansu tare a dandalin sada zumunta ta Instagram inda za a gano su cikin fara'a da annashuwa. 

Kenya ta ce mazajen nata biyu suna zaman lafiya, su kan yi yawancin harkokin su ba yau da kullum kamar gyaran mota da wasu abubuwan tare. Ta kuma ce ba gaskiya bane ikirarin da ake yi cewa maza sun fi mata sha'awa sai dai kawai an daɗe ana dakushe mata ne shi yasa suke danne sha'awarsu. 

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Matar da ke auren maza biyu a lokaci guda kuma suke zaune gida ɗaya (Hotuna)"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?