
Kai makaryaci ne, kalamanka na da hadari ga Najeriya: DSS ga Obadiah Mailafiya
Hukumar ta ce lokacin da yake ofishinsu dake Jos, ya karyata maganar da yayi amma da ya samu yanci sai ya fara cewa yana kan bakansa, Vanguard ta ruwaito. A ranar Laraba, Hukumar DSS sammaceshi ne kan jawabin da yayi inda ya bayyana cewa daya daga cikin tubabbun yan Boko Haram da aka saki ya fada masa cewa wani gwamnan Arewa ne shugaban yan Boko Haram.
Daga baya ta sakeshi bayan sa'o'i bakwai yana amsa tambayoyi. DSS tace: "Abin takaici shine Mailafiya, wanda yayi ta bamu hakuri yayinda ya ziyarci ofishin hukumar dake jihar Plateau kan jawabin karyansa, amma daga baya ya sanar da duniya cewa yana kan bakansa."
"Hakazalika, hukumar tana gargadin jama'a, wadanda suke amfani da sunan siyasa wajen furta kalaman batanci su daina."
A bangare guda, Hukumar lura da kafafen yada labarai a Najeriya NBC, a ranar Alhamis ta ce za ta fara hukunta duk tashar watsa labaran da ta sabawa dokokinta. Ta gargadi kafafen watsa labarai cewa su fahimci dokoki da ka'idojin sana'ar. Diraktan hukumar NBC na jihar Legas,
Chibuike Ogwumike ya bayyana hakan a takardar da aikewa manema labarai. Hakazalika, hukumar NBC ta ci tarar wani gidan radiyo da ke jihar Legas Naira miliyan biyar. NBC ta bayyana cewa an ci tarar gidan radiyon mai suna 'Nigeria Info 99.3FM' saboda yin amfani da wani shirinsu wajen yada labarai marasa tushe da kan iya haifar da hargitsi da tsana a tsakanin jama'a.
Gidan radiyon 'Nigeria Info' ne ya fara yada hirar da tsohon dan takarar shugaban kasa, Obadiah Mailafia, ya yi zargin cewa wani gwamnan arewa ne ya ke shugabantar kungiyar Boko Haram.
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kai makaryaci ne, kalamanka na da hadari ga Najeriya: DSS ga Obadiah Mailafiya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?