
Jinin Haila: Abubuwan da suka kamata ki sani kan al'ada da ɗaukar ciki
A wasu lokutan matsalar rashin haihuwa ga ma'aurata na samo asali ne daga rashin fahimta kan batutuwa daban-daban da suka shafi yanayin jikin mace, ciki har da ovulation, wato lokacin da ƙwan haihuwar mace ke ƙyanƙyashewa.
Galibi mutane sun san lokacin jinin haila wanda mace ke yi a kowane wata, sai dai kalilan ne kawai suka fahimci lokacin da ƙwan haihuwa ke ƙyanƙyashewa, wanda hakan na faruwa ne kwana 14 kafin zuwan jinin haila
Ovulation shi ne fitar ƙyanƙyashewa.wai daga mahaifar mace zuwa wuyan mahaifa wanda ya ke ƙyanƙyashewa idan ya hadu da maniyin namiji a lokacin jima'i.
A cewar ƙwararru kan haihuwa, ovulation shi ne lokacin da mace ke ɗaukar ciki a lissafin lokacin ganin hailarta.
Dokta Joseph Akinde likitan haihuwa ne, kuma ya yi bayyanin cewa ''idan namiji da mace suka sadu kwana guda zuwa biyu kafin ovulation, mace za ta ɗau ciki.''
Kamar dai yadda kowace mace ke da lokacin ganin hailarta, haka zalika kowace mace na da lokacin da take fitar da ƙwan haihuwa.
Akinde ya yi bayanin cewa: ''Misali, idan kina ganin jinin haila bayan kowane kwana 26, sannan hailar na zuwar miki ranar 2 ga watan Agusta,(2020) ki sake ganin wata ranar 29 ga watan Agusta, to ranar fitar ƙwanki ko ovulation shi ne 15 ga watan Agusta.''
''Wasu mata na ganin jinin haila bayan kwana 26, wasu kuma 32.''
''Macen da ke ganin haila bayan kowane kwana 24, ƙwanta na fita a ranar ta 14, yayin da su kuma masu ganin haila bayan kwana 32, ƙwansu na fita a rana ta 18.''
Da fari, kowace mace ana haifarta da ƙwayaye miliyan daya zuwa miliyan biyu.
Idan ta kai lokacin balaga, ƙwan na fita a kowane wata a matsayin haila idan macen ba ta sadu da namiji ba.
Alamomin fitar ƙwai ko Ovulation
A cewar Dokta Akinde, kwararan likita a asibitin Living Spring da ke Legas, '' wasu mata na ganin digon jini, rikewar mara ko zugi na miniti 1 zuwa sa'o'i 24 amma dai baya wuce sa'a 24.''
Wata mata da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida cewa ''a lokacin fitar ƙwaimamana na kumbura da nauyi.''
Sai dai ba duk mata ke fuskantar abu iri guda a lokacin fitar ƙwai ko yanayin ya zo musu guda ba ko kuma lissafin lokacin fitar ƙwan ya zo daya.
Dabarun gane ko lissafin ovulation
Ma'aurata da ke neman haihuwa na iya amfani da lokacin fitar kwai don cimma burinsu
Kamar yadda Dokta Akinde ya bayyana, akwai hanyoyi da dama na lissafa lokacin fitar ƙwai ko ovulation.
Sun haɗa da:
1. Riƙe lokacin zuwan jinin al'ada ko haila
A tanadi ɗan littafi ko kalandar rubuta lokacin zuwan al'ada
Duk lokacin da aka ga al'ada, a rubuta a kalanda
Rubutu lokacin zuwan al'ada na gaba a kalanda
Ki riƙe giɓin da kika samu tsakanin al'adarki ta farko zuwa al'adarki ta gaba
Ranakun fitar ƙwan mace akasari kwanaki 14 ne kafin zuwan al'adarta, ko ya yanayin al'adar ko lokacin zuwansa yake.
2. Yanayin ɗumin jiki a lokacin hutawa
A cewar Dokta Akinde, mace na iya amfani da na'urar auna zafin jiki ta thermometer a ƙarƙashin harshenta lokacin da ta farka daga barci kafin ta sauka daga gado.
''Yayin da take ɗaukar yanayin jikinta tana adanawa, za ta fahimci cewa wata rana ɗumin jikin zai sauka kadan kafin ya sake dagawa. Wannan shi ne lokacin ovulation.''
3. Amfani da abin gwaji
SOURCE: bbchausa/
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Jinin Haila: Abubuwan da suka kamata ki sani kan al'ada da ɗaukar ciki"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?