--
Duba 'Yan bindiga suka kashe wani ɗan kasuwa a Kaduna cikin gonarsa

Duba 'Yan bindiga suka kashe wani ɗan kasuwa a Kaduna cikin gonarsa



Mutanen garin Udawa a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna sun shiga ruɗani yayin da wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka kashe wani ɗan kasuwa a gonarsa. An bayyana cewa sunan marigayin ɗan kasuwan Malam Jafaru Bello.

Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan bindigan sun kai masa hari ne a lokacin da ya tafi gonarsa a wani gari mai suna Goluwa a safiyar ranar Laraba. An kuma gano cewa ƴan bindigan sun yi awon gaba da wasu manoma uku daga gonarsa a ranan da suka kashe shi.

Garin Udawa yana da iyaka da ƙaramar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna. Wani jagoran al'umma a garin, Malam Muhammadu Umaru wanda ya tabbatar wa majiyar Legit.ng afkuwar lamarin ya ce wanda abin ya faru da shi makwabcinsa ne.

Malam Umaru ya ce, "Irin wannan abin bai taɓa faruwa ba; ta baya aka kashe shi. Makwogoronsa ne kawai ya rage da sun datse kansa. Jafaru makwabci na ne kuma ɗan kasuwa ne mai mata hudu da ƴaƴa 12. Ƴan bindiga sun masa kisar rashin tausayi a gonarsa a safiyar ranar Laraba.

Sun kuma sace wasu manoma uku sun tafi da su." Ya ce ƴan bindigan su kan harbi waɗanda suka kama ne amma yanzu yankan rago suke musu wadda hakan ya jefa ƴan kauyen cikin damuwa. Mai magana da yawun ƴan sandan jihar bai sama wayarsa ba.

Amma kwamishinan ƴan sandan jihar, CP, Umar Musa Muri ya ce ba zai iya tabbatar da afkuwar lamarin ba a lokacin da aka tuntube shi. Ƙaramar hukumar Chikun tana ɗaya daga cikin garuruwan da ake fama da matsalar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Duba 'Yan bindiga suka kashe wani ɗan kasuwa a Kaduna cikin gonarsa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?