
Da duminsa: An samu gawar wata matar da mijinta ya kulle tsawon kwana 3 a Kano
Hotuna daga TVC News ya nuna gawar mata da cikin dakin da kuma yadda mutane sukayi cincirindo a wajen gidan. SaharaReporters ta tattaro cewa wannan abu ya faru ne a Mariri Quarters dake cikin garin Kano. Makwabta ne suka sanar da yan sanda yayinda suka gano gawar da ta fara rubewa
Wannan na faruwa kwana daya bayan gano mutum dan shekara 55 da aka daure na tsawon shekaru 30 a cikin gida a Kano. Jamian yan sanda da yan kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Network ne suka ce Muhammad, mazaunin Kofar Fada a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano a ranar Alhamis.
An ce an daure shi ne saboda yana fama da tabin hankali. Muhammad ya ce ya yi farin ciki da aka cece shi daga halin da mahaifinsa ya jefa shi ciki. Hakazalika a ranar 13 ga Agusta, yan sanda a jihar Kano har ila yau sun ceto wani matashi mai shekaru 32, Ahmad Aliyu, wanda mahaifinsa da kishiyar mahaifiyarsa suka kulle tsawon shekaru bakwai a jihar Kano.Yan sandan sun kai wannan farmaki ne daren Litinin a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano. Mutumin, wanda hoto da bidiyo suka nuna yana cikin mawuyacin hali ya kwashe kwanaki babu abinci, babu ruwan sha sai dai shan fitsarinsa, HumAngle ta ruwaito.
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Da duminsa: An samu gawar wata matar da mijinta ya kulle tsawon kwana 3 a Kano "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?