Bidiyo: Wata mata ta daure dan kishiya tsawon shekara biyu a turken tumaki
Monday, 10 August 2020
Comment
Wata mata ta daure yaro maraya mai shekaru 10, mai suna Jibril Aliyu, na tsawo shekaru biyu a garken tumaki ba tare da abinci isasshe ba a jihar Kebbi. Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, matar uban yaron ta dinga yi mishi tamkar ba dan Adam ba bayan rasuwar mahaifiyarsa.
Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani a sa'o'in farko na ranar Litinin, wanda ke nuna yaron a rame har baya iya tashi tsaye saboda yunwa. Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, an damke wacce ake zargin yayin da aka kwantar da yaron a asibitin tunawa da Yahaya da ke Birnin Kebbi.
Wani bidiyo wanda ake zargin an daukesa a ofishin 'yan sanda a jihar, ya bayyana wacce ake zargin tana bayani ga 'yan sanda inda take musanta daure yaron. Kamar yadda wata ma'abocin amfani da Facebook, Tukur Tacha, ya wallafa, ya ce mahaifiyar yaron ta rasu a shekarun da suka gabata kuma ana zargin marikiyarsa da ciyar da shi da ragowar abinci da kuma kashin tumaki.
Wata ma'abociyar amfani da kafar sada zumunta ta Facebook mai suna Maryam Shetty, ta kushe halayyar matar da ta zarga da rashin nuna nadama tare da kwatanta ta da shaidaniya. Ta ce: "Bidiyon wata shidaniyar mata da ta daure maraya na tsawon shekaru biyu kamar akuya gaskiya ne.
Yana fama da yunwa don da ragowar abinci da kashin dabbobi take ciyar da shi. Rashin tausayi..." A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kebbi, ya tabbatar da kamen wacce ake zargin tare da cewa matar tana hannun 'yan sanda. Kamar yadda yace, idan aka kammala bincike, za a gurfanar da ita a gaban kotu.
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Bidiyo: Wata mata ta daure dan kishiya tsawon shekara biyu a turken tumaki "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?