
Bidiyo: Budurwa ta ki karbar kyautar motar N6.6m saboda bata son fentin jikinta
Saurayin matar ya yi niyyar bata mamaki ta hanyar saya mata mota kirar 'G Wagon' a kan miliyan N66.6 tare da yi mata kwalliya da jajayen kyalle kafin a kaiwa masoyiyarsa ita a matsayin kyauta. Domin kara armashin dabararsa ta bawa masoyiyarsa mamaki, saurayin ya yi amfani da kyalle wajen rufe idanunta tare da kama hannunta zuwa wurin da aka ajiye motar.
Bayan an bude idon budurwar domin ta yi kwalli da motar da saurayinta ya siya mata, sai kawai ta fashe da kuka. Sabanin tunanin jama'a a kan cewa tana kukan jin dadi ne, sai ta fada cikin kuka cewa ba za ta karbi kyautar motar ba saboda ba irin kalarta take so ba.
Saurayinta, wanda ke tsaye domin ganewa idonsa irin murnan da za ta yi na samun kyautar bazata ta motar alfarma, ya matukar girgiza da jin cewa ba zata karbi kyautar motar ba saboda kawai bata son fentinta.
Cikin murna da zumudi saurayin ya shiga cikin gidansu tare da katsewa budurwar uzurinta domin ta fito ta ga motar da ya sayo mata ba tare da saninta.
Shi kansa saurayin ya kasa boye mamakinsa bayan masoyiyarsa ta sanar da shi cewa motar ta yi amma ba za ta iya karba ba saboda ba ta son irin kalar wacce ya sayo. Cikin kuka ta koma cikin gidansu ta na maimaita cewa; ''ba wannan kalar nake so ba, ba irinta na ke so ba,".
Kalli faifan bidiyon a kasa;
SOURCE: legit.ng
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Bidiyo: Budurwa ta ki karbar kyautar motar N6.6m saboda bata son fentin jikinta "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?