--
Babban jigon Darikar Tijjaniya ya kwanta dama

Babban jigon Darikar Tijjaniya ya kwanta dama



Allah Ya yi wa babban malamin addinin Musulumcin nan na kasar Senegal kuma Babban Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass, Sheikh Khalifa Ahmad Tijjani bin Ali Cisse, rasuwa.

Shaikh Khalifa Ahmad Tijjani ya rasu ne a kasar ta Senegal a daren Lahadi bayan ya yi fama da jinya.

An haifi marigayin ne ranar 1 ga watan Janairun 1955, kuma kafin rasuwarsa shi ne jagoran mabiya darikar Tijjaniyya wadanda aka kiyasta sun kai kusan miliyan 100 a fadin duniya.

Malamin ya hau khalifanci ne bayan tarbiyar da ya samu daga jagororin darikar ta Tijjaniya, Shaikh Ibrahim Inyass, da Shaikh Sayyidi Ali Cisse, da Shaikh Hassan bin Ali Cisse.

Marigayin da ga Fatima, diyar Shaikh Ibrahim Inyass ta farko, da Shaikh Sayyidi Ali Cisse, mafi kusa da shi a cikin dalibansa.

Nan ba da jimawa ba ake sa ran iyalansa za su sanar da lokacin jana’izarsa a bisa tanade-tanaden addinin Musulunci.

SOURCE: https://aminiya.dailytrust.com.ng/

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Babban jigon Darikar Tijjaniya ya kwanta dama"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?