
An kwace gawar wani jariri a wajen wata mahaukaciya bayan shafe sama da mako 1 tana yawo da shi a bayanta
Sai da aka tara matasa masu yawa kafin a samu a yiwa mahaukaciyar wayo aka kwace jaririn aka binne a makabarta Wata mata da aka tabbatar da cewa mahaukaciya ce ta shafe sama da mako daya tana yawo da gawar wani jariri a bayanta,
mutane sun gano hakan ne bayan warin gawar jaririn ya fara damunsu. Matar an ganta a ranar Talata, 18 ga watan Agusta, dauke da gawar yaron a karamar hukumar Effium Ohaukwu dake jihar Ebonyi.
An ruwaito cewa matar ta isa wannan gari ne watanni kadan da suka wuce daga wani wuri da ba a san ko ina bane, inda ta fara zama a wani kangon gida.
Mutane basu san da zamanta a wannan waje ba har sai da mutane suka fara jin wani wari a duk lokacin da ta wuce daga gabansu, sai suka sanar da 'yan sanda bayan an bincika aka gano cewa warin na fitowa daga jikin yaron dake goye a bayanta ne.
Wata majiya ta sanar da jaridar Punch cewa: "Yan sandan sun sanar da wasu cibiyoyi guda biyu dake yankin, cibiyoyin guda biyu sun tara matasa domin kwace jaririn daga hannun mahaukaciyar.
"Sai dai matar taki yadda a kwace jaririn, hakan yasa aka yi ta fama da ita. Sai da matasan suka yi mata wayo sannan suka samu suka kwace gawar jaririn. "Gawar yaron tuni har ta fara rubewa a bayanta, saboda tana goye da shi fiye da mako daya. Matasan sun kwace gawar daga wajenta inda suka binne shi a makabarta a ranar Talata."
Agbo Sunday ya tabbatarwa da jaridar Punch cewa an binne gawar jaririn a ranar Talata kuma tuni mutane sun cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba a baya. "Mutane su koma su cigaba da kasuwancin su, saboda komai ya wuce an dauki mataki akan lamarin. An binne gawar jaririn a ranar Talata," cewar shi.
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "An kwace gawar wani jariri a wajen wata mahaukaciya bayan shafe sama da mako 1 tana yawo da shi a bayanta "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?