
An damke fasto da ta sace jinjira a Akwa Ibom
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, CSP Nnudam Fredrick, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a babban birnin jihar, Uyo. Ya ce wasu da ake zargi da hannu cikin satar yaran sun hada da Esther Esin, 41 yar garin Eyo Abasi, a karamar hukumar Oron, Mrs Rose Asuquo, 32, yar garin Mbak Atai, karamar hukumar Itu, da Ubong Akpan, 42, dan garin Mbak Atai, daga karamar hukumar Itu.
Saura sun hada da Mr Samuel Idobo, 40, mazaunin Ikot Asukpong, a karamar hukumar Ibiono Ibom da Mrs Eno Peter, 40, yar garin Ikot Andem Itam, da ke karamar hukumar Itu. "Jajircewar da rundunar yan sandan ke yi domin magance matsalar satar yara ya fara samun nasara inda aka damke gawurtattun masu satar yara a jihar,"
in ji Fredrick. Fredrick ya ce an yi nasarar kama yan kungiyar masu satar yaran ne sakamakon sahihan bayannan sirri da rundunar ta samu a watan Yuni. Ya ce shugaban kungiyar, Rose Ekpenyong, ta hada baki da sauran wadanda ake ambaci sunansu a matsayin wadanda ake zargi wurin sayar da wata jinjira a shekarar 2018.
Fredrick ya ce faston ta amsa laifin ta inda ta ce an saya jinjiran ne domin a bawa yar uwar ta mai suna Esin. "Hakan ya sa jami'an hukumar suka bazama suka kamo ta sannan suka ceto jinjirar," in ji shi. Fredrick ya yi kira da alumma su cigaba da taimakawa rundunar da bayanai masu amfani da za su taimaka musu wurin kama masu satar yara da safarar su.
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "An damke fasto da ta sace jinjira a Akwa Ibom "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?