
An bude jigilar jiragen sama zuwa kasashen waje
Da almurun Litinin 17 ga Agusta 2020 ne ministan ya sanar da hakan ta shafinsa na Twitter cewa za a ci gaba sufurin kasa da kasa ne daga ranar 29 ga watan Agusta.
“Za mu fara da Legas da Abuja kamar yadda muka yi a lokacin bude sufurin jirage na cikin gida. Nan gaban za a sanar da tsare-tsaren da kuma matakan da aka tanada. Muna godiya bisa hakurin da kuka nuna”, inji shi.
Wakilinmu ya ruwaita ministan na sanar da haka a lokacin taron jawabin kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19.
Ya ce idan aka bude filayen bayyan mako biyun masu zuwan, za a ci gaba da bin sauran matakan kariya da suka hada da bayar da tazara da dangoginsu.
Tun a watan Fabrairu Gwamnatin Tarayya ta rufe dukkannin tafiye-tafiyen jiragen sama da na kasa domin dakile yaduwar cutar COVID-19.
Cutar ta fara bulla a Najeriya ne a jikin wani bako dan kasar Italiya da ya shigo kasar da ita ta filin jirgi na Legas.
Ba a gane yana dauke da cutar ba sai bayan sa’o’i kuma daga nan aka yi ta samun karuwar masu ita a kasar.
SOURCE: AMINIYA DAILY TRUST
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "An bude jigilar jiragen sama zuwa kasashen waje"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?