--
Zargin biliyan N81.5: Pondei ya sume a gaban kwamiti bincike

Zargin biliyan N81.5: Pondei ya sume a gaban kwamiti bincike




Mukaddashin Shugaban Hukumar da ke kula da Habbaka Neja Delta (NDDC) Farfesa Kemebradikumo Pondei, ya fadi sume a gaban kwamitin bincike na Majalissar Wakilai.

Pondei a suma ne bayan da fara amsa tambayoyin da Kwamitin binciken ya fara yi masa a ranar Litinin.

An fitar da shi a guje daga cikin dakin taron da ake yi masa tambayoyi a kan facaka da kudaden hukumar.

A makon da ya gabata, Pondei da shugabannin gudanarwar NDDC sun fice daga dakin taron bisa korafin cewa ba za su amince Shugaban Kwamitin na Majalisar ya jagoranci binciken ba.

Ya kafa hujja da cewa Shugaban Kwamitin Majalisar shi kansa akwai zargin rashawa a kansa.

A ranar Litinin din ne kuma Shugaban Kwamitin ya sauka domin bayar da damar shugannin hukumar su kare kansu a gaban Kwamitin.

Kawo yanzu an ce Pondei yana hannun likitocin suna duba lafiya.

Source: https://aminiya.dailytrust.com.ng/

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Zargin biliyan N81.5: Pondei ya sume a gaban kwamiti bincike"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?