
'Ya'yan El-Rufai sun caccaki Atiku bayan dan sa ya yi wa El-Rufai habaici
Wednesday, 1 July 2020
Comment
ROHOTON: LEGIT.NG
'Ya'yan Gwamna Nasir El-Rufai, Bashir da Bello, sun caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, bayan daya daga cikin 'ya'yansa ya yi wa mahaifinsu habaici. Dan Atiku Abubakar mai suna Mustapha, ya yi martani a inda El-Rufai ke shawartar iyaye da su koyar da 'ya'yansu girmama mata tun suna kanana.
A cewar gwamnan, hakan ne kadai zai iya dakile annobar fyade da ke tashe a kwanakin nan. Babu kakkautawa Mustapha Atiku ya je yayi tsokaci a kasan wallafar inda yace "Abun mamaki".
The irony... https://t.co/kgvqM6N9RI— Alhaji Mustapha Abu Bakr (@HHMustaphaAA) June 29, 2020
— isa Koki (@isaKoki4) June 30, 2020
Babu jimawa kuwa Bashir El-Rufai ya yi martani inda ya kira sunan Atiku tare da cewa "Irin wannan abun mamakin ne ke faruwa a duk lokacin da mahaifinsa ya yi magana a kan rashawa." Ba tare da bata lokacin ba, Bello El-Rufai ya je ya yi nasa martanin mai zafi inda yace, "Bash, zancen ana yinsa ne a kan darajar mata ba luwadi ko rashawa ba.
"Kada ka damu da sabon angon, tsohon abokin naka ya yi tunanin a yanzu yana fadar shugaban kasa inda yake da daman kaiwa ga NNPC kai tsaye."
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "'Ya'yan El-Rufai sun caccaki Atiku bayan dan sa ya yi wa El-Rufai habaici"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?