
Yauce Ranar ƙarshe a Premier League : Labarin Wasanni
Sunday, 26 July 2020
Comment
A yammacin yau za a yi ta ta ƙare a wasan ƙarshe na kakar Premier League ta bana, inda za a buga wasa 10 a lokaci guda - ƙarfe 4:00 agogon Najeriya.
Sai dai hankali zai fi karkata kan fafatawa uku; Manchester United vs Leicester City, Chelsea vs Wolves, Tottenham vs Crystal Palace.
Me ya sa hankali zai fi karkata kan waɗannan wasannin?
Abin da Man United ke buƙata: Man United za ta samu shiga gasar Zakarun Turai ta Champions League idan ta doke Leicester City. Idan kuma ta yi rashin nasara, to sai an doke Chelsea sannan take da damar shiga gasar
Abin da Leicester City ke buƙata: Idan Leicester ta ci Man United za ta samu zuwa Champions League. Idan aka yi kunnen doki kuma to sai Chelsea ta yi rashin nasara sannan za ta samu gurbin shiga gasar
Abin da Chelsea ke buƙata:Chelsea za ta je Champions League idan ta ci wasa. Idan kuma ta yi rashin nasara, to sai Man United ta doke Leicester sannan za ta samu gurbin shiga gasar
Abin da Tottenham ke buƙata: Idan Wolves ta yi rashin nasara a hannun Chelsea to Tottenham za ta buƙaci maki ɗaya ne kacal domin ta ƙare a mataki na shida, wanda zai ba ta damar zuwa gasar Europa League.
Idan ta rasa maki ɗayan kuma, to sai ta jira ta ga wanda zai lashe kofin FA
Abin da Wolves ke buƙata: Idan Wolves ta ci wasa za ta samu gurbin shiga Europa. Idan kuma ta yi rashin nasara to za ta ƙare a mataki na bakwai sannan ta jira ta ga wanda zai lashe kofin FA
Article share tools
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Yauce Ranar ƙarshe a Premier League : Labarin Wasanni"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?