Yanzu yanzu: Mohammed Umar ya zama sabon shugaban EFCC
Friday, 10 July 2020
Comment
Gwamnatin Najeriya ta nada Mohammed Umar a matsayin sabon mukaddashin shugaban EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
An nada Mohammed Umar a matsayin sabon mukaddashin shugaban EFCC ne bayan dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar.
Sanarwar da Umar Jibrilu Gwandu, mai magana da yawun Ministan Shari'ar kasar Abubakar Malami ya fitar ranar Juma'a ta ce "Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Ibrahim Magu daga mukamin mukaddashin shugaban EFCC nan take, domin kwamitin da shugaban ya nada ya gudanar da bincike a kansa ya samu damar yin hakan ba tare da shamaki ba."
A cewar sanarwar, Shugaba Buhari "ya kuma amince daraktan ayyuka na EFCC, Mohammed Umar, ya karbi ragamar tafiyar da hukumar har lokacin da za a kammala binciken da ake yi da kuma marni na gaba kan batun".
SOURCE: BBCHAUSA
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Yanzu yanzu: Mohammed Umar ya zama sabon shugaban EFCC"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?