
Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana a kan tuhuma da dakatar da Magu
Saturday, 11 July 2020
Comment
![]() |
Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana a kan tuhuma da dakatar da Magu. Hoto daga Premium Times Source: UGC |
A duk lokacin da ake zargin shugaban wata hukuma, a kan bukacesa da ya dakata da aiiki don a samu damar yin bincike ba tare da wata matsala ba. "EFCC bata dogaro da yanayin mutum, a don haka bata sassauta wa kowa. Dakatar da Magu kuwa ya bai wa hukumar damar sauke nauyinta ba tare da wani cikas ba.
"EFCC na da zakakurai, jajirtattun ma'aikata maza da mata masu fatan kiyaye dukkan dokokin kasar nan tare da mika duk wanda ya zo da almundahana gaban hukuma.
Ta kowanne fanni ana kokarin tabbatar da shi. Ya kara da cewa, masu kallon bincikar Magu da ake yi a matsayin wata koma baya ga yaki da rashawa, toh a gaskiya sun kauce. Bincikar Magu na nuna cewa da gaske ana yaki da rashawa a bayyane ba tare da boye-boye.
A karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnati, babu wanda zai zamo zababben ko kuma wanda ya fi karfin hukuma, Magu bashi da wata kariya. Babu wata gwamnati a tarihin kasar nan da ta taba yin abinda wannan gwamnatin tayi na yakar rashawa karara.
SOURCE: LEGIT.NG
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana a kan tuhuma da dakatar da Magu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?