Yanzu Yanzu: Buhari ya shiga ganawar sirri da Jonathan
Tuesday, 21 July 2020
Comment
Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga labule da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan - Sun shiga ganawar ne cikin sirri a fadar Villa da ke Abuja Zuwa yanzu dai ba a san ainahin dalilin ganawar tasu ba
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a fadarsa da ke Abuja. Goodluck Jonathan ya isa fadar shugaban kasar a safiyar yau Talata, 21 ga watan Yuli. Har a halin yanzu ba a san abinda suke tattaunawa ba saboda taron na sirri ne suka shiga.
Sai dai an tattaro cewa ganawar baya rasa nasaba da karramawar da shugaba Buhari ya yi wa tsohon Shugaban kasar. Idan za ku tuna, a baya Legit.ng ta rahoto cewa duk da banbancin siyasa da ke tsakani, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sanya wa filin jirgin kasa na Agbor sunan wanda ya gada, Goodluck Jonathan.
Rotimi Amaechi, ministan sufuri, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 18 ga watan Yuli ta wallafar Twitter da hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi yayi. Ministan sufuri ya ce titin jirgin kasa na Itakpe zuwa Warri daga yanzu za a dinga kiran shi da na Goodluck Jonathan.
Rotimi Amaechi, ministan sufuri, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 18 ga watan Yuli ta wallafar Twitter da hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi yayi. Ministan sufuri ya ce titin jirgin kasa na Itakpe zuwa Warri daga yanzu za a dinga kiran shi da na Goodluck Jonathan.
Amaechi ya ce za a kaddamar da babban aikin ta yanar gizo kuma babban abinda za a fifita shine sufurin kayayyaki ballantana yadda titin jirgin ya ratsa ta Ajaokuta. "Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kiran filin jirgin kasa na Agbor wanda ya fara daga Itakpe zuwa Warri, da sunan Goodluck Jonathan. Daga yanzu sunan wurin filin jirgin kasa na Goodluck Jonathan,"
Tolu Ogunlesi yace. Da aka bukaci sanin lokacin da za a kaddamar, ya ce: "Wannan ya dogara neda lokacin da ma'aikatar ta samu yarjewar shugaban kasa. Muna tunanin kaddamar da shi ta yanar gizo saboda korona."
A gefe guda, mun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara gwajin sabbin jiragen kasa da ta sayo daga kasar China, kamar yadda ministan sufuri, Rotimi Amaechi, sanar da yammacin yau, Juma'a. Da ya ke sanar da hakan a shafinsa na tuwita, Amaechi ya bayyana cewa an fara gwajin sabbin jiragen a kan sabbin titunan jirgin kasa da aka gina daga Itakpe zuwa Warri.
Source: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Yanzu Yanzu: Buhari ya shiga ganawar sirri da Jonathan "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?