--
Yanda aka kama gandiroba yana yiwa mai cutar Coronavirus fyade

Yanda aka kama gandiroba yana yiwa mai cutar Coronavirus fyade




‘Yan sandan kasar Kenya sun kama wani gandiroba da laifin yiwa wata budurwa mai dauke da cutar coronavirus fyade a cikin wajen da aka killace su, inda aka bar shi yayi gadi, cewar wani rahoto da rundunar ‘yan sanda ta fitar.

Wannan shine dai babban lamari da ya faru a gwamnatin kasar dan gane da masu cutar coronavirus a yankin Gabashin Afrika.

Wannan lamari dai an bayyana cewa zai sanya tsoro ga mutann da suke dauke da cutar wajen gabatar da kansu domin ayi musu gwajin wannan cuta koda kuwa suna da ita.

A farkon wannan shekarar dai akwai korafi da yawa da aka dinga fitarwa daga cibiyoyin da ake killace masu cutar da suka hada da rashin isashen abinci, ruwan sha da kuma kyakkyawan mahalli ga wadanda aka ajiye su a ciki.

A watan Maris, mahukunta sun ce suna bincike akan wani kisan kai da aka yi a cikin daya daga cikin cibiyoyin. Wannan sabon lamari dai ya faru a wani gari dake iyakar yammacin Busia, inda ‘yan sanda da gandirobobi suke gadi, a rahoton da ‘yan sanda suka bawa Reuters.

An ruwaito cewa daya daga cikin abokanan aikin gandirobobin yana magana da daya daga cikin marasa lafiyan, sai ya fita yaje ya sanar da sauran jami’an halin da ake ciki.

“Sun jiyo ihu da surutai na fitowa daga cikin wurin da ake killace matan,” cewar rahoton. Bayan zuwa jami’an sun tarar da cewa duka sauran marasa lafiyan sun fito suna korafin cewa daya daga cikin gandirobobin yana ciki yana yiwa daya daga cikinsu fyade.

An kama jami’in inda aka rufe shi a cikin wajen, kamar yadda rahoton ya bayyana. Kakakin rundunar ‘yan sandan bai ce komai ba a lokacin da aka kira shi dangane da lamarin.

Source: PRESSLIVES.COM

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanda aka kama gandiroba yana yiwa mai cutar Coronavirus fyade"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?