--
‘Yan ta’addan Boko Haram sun datse kan Jagororin da ke yaki a tafkin Chad

‘Yan ta’addan Boko Haram sun datse kan Jagororin da ke yaki a tafkin Chad




Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa sababbin shugabannin kungiyar ‘yan ta’addan ISWAP da majalisar shura sun hallaka wasu manyan jagororin yakin ‘yan ta’addan. Daga cikin wanda aka kashe har da wani babban mayakin kungiyar, Baba Kaka, wanda ya shafe shekaru hudu ya na jagorantar ta’adin da ISWAP ta ke yi a cikin yankin tafkin Chadi.

Bayan Amir Baba Kaka, babban Alkalin ISWAP ya yankewa shehin malamin kungiyar, Ba’a Masta, da wasu mutane 14 hukuncin kisa, kuma ana sa ran fille kansu bayan bikin idi. Rahotanni sun ce sabon shugaban ISWAP, Amir Abubakar Lawan ya nada Amir Goni Maina a matsayin gwamnan shiyyar Tunbu bayan an yankewa Baba Kaka hukuncin kisan kai.

A ranar Lahadi, 26 ga watan Yuli, aka datse kan tsohon shugaban a dajin Kwalaram tare da wasu manyan sojojinsa; Amir Muhammed Lawal wanda aka fi sani da Abba Lawal da Amir Musa. “Bincike da hukuncin kisan da aka yankewa Amir Baba Kaka da yaransa biyu ya dauki tsawon makonni hudu.”

Alkalin alkalan ISWAP, Amir Malumma da ‘yan majalisarsa; Malam Ibrahim, da babban Malamin Boko Haram, Malam Sa’ad da Bako Fulgori su na cikin wadanda su ka yi wannan shari’a. Rahoton ya kara da cewa an kashe Kaka ne domin Amir Abubakar Lawan da babban na-kusa da shi, Abu Musab Al-Barnawi su kara samun karfin iko a tafiyar ‘yan ta’addan.

“Ana fahimtar mafi yawan sojojin da aka kashe ko aka yankewa hukuncin kisa sun taka rawar gani wajen kifar da gwamnatin ‘dan tsohon shugaban Boko Haram, Abu-Musab Al-Barnawi.” Shari’ar da aka yi ya nuna cewa Alkali ya samu Amir Baba-Kaka da aikata manyan laifuffuka. “Wadannan laifuffuka sun hada sabawa umarni, rashin adalci, satar dukiya, cin kudin haraji, tunzura cin amana, da kuma kisan gilla."

"Sauran laifuffukan sun hada da gaza rike iyakarsa a lokacin da ya ke gwamnan Tumbus.” ISWAP ta na zargin cewa rashin kokarin tsohon gwamnan ya sa sojojin MNJTF su ka samu galaba a kan Boko Haram

SOURCE: LEGIT.NG

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "‘Yan ta’addan Boko Haram sun datse kan Jagororin da ke yaki a tafkin Chad "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?