'Yan Siyasan Dake Adawa Da Gwamnatinmu Su Suke Daukar Nauyin Ta'addacin Da Ake Yi A Katsina, Cewar Gwamna Masari
Monday, 20 July 2020
Comment
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewa masu yi wa jam'iyyar APC zagon kasa da bakin ciki sune ummul aba'isin daure wa masu kai hare-haren ta'addanci da na Boko Haram gindi a yanki Arewa maso Yammacin Nijeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin gangamin taron yan jam'iyyar APC tun daga matakin mazabu har zuwa ka kananan hukumomi da kuma jigajigan jam'iyyar APC da ya wakana a ranar Lahadi don neman dinke barakar dake cikin jam'iyyar.
Gwamnan ya ce yan siyasa sune uwa da makarbiyar kai hare-haren ta'addanci da na Boko Haram domin ganin sun dushe hasken jam'iyyar APC wajen gazawa don su sami damar lashe zabe mai zuwa na 2023, kamar yadda Katsina Daily Post News ta fassaro daga Daily Post
"Mafi yawan kai hare-haren ta'addanci da na Boko Haram a Arewacin Nijeriya yan siyasa ne ke daukar nauyinsa wadanda suke makiyan jam'iyyar APC ne tun daga matakin jiha har zuwa tarayya. Inji Masari
"A lokacin mulkin Goodluck Jonathan an sami yawaitar tashe-tashen bama-bamai a Mai'duguri , da Kano harma da babban birnin tarayya Abuja.
" A tashin bam din Kano ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 500, an kulle masallatai da Coci-coci, da hanyoyi saboda rashin tsaro, amma yau Allah Ya tsare mu daga irin wadannan rashin tsaron, amma mun manta.
" A yau yan siyasar dake neman tsayawa takarar 2023 suke daukar nauyin kai hare-haren ta'addanci" inji gwamna Masari
Gwamnan ya bayyana cewa wadannan 'yan siyasar sun yi imanin cewa APC ta amshe mulki a wajen PDP saboda rashin tsaro, don haka suke son su aikata irin haka a mulkin APC.
SOURCE: SHAFIN RARIYA NA FACEBOOK
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "'Yan Siyasan Dake Adawa Da Gwamnatinmu Su Suke Daukar Nauyin Ta'addacin Da Ake Yi A Katsina, Cewar Gwamna Masari"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?