--
'Yan bindiga sun kashe mutum 18 a gidan biki a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe mutum 18 a gidan biki a Kaduna


Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 18 da kuma jikkata wasu 30 a gidan biki.

An kai harin ne a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna kan masu bikin aure a kauyen Kukun-Daji.

Lamarin dai ya faru ne a jiya Lahadi da tsakar dare. Bayanai na cewa ango da amaryar da ake bikinsu, sun tsira daga harin.

Wani shugaban al'umma daga yankin Kaura, Jonathan Asake ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun bude wuta ne yayin da mutane ke ta cashewa, sannan daga bisani suka tsere.

Jonathan ya ce nan take mutum 15 suka mutu - sauran uku kuma sun mutu ne a asibiti lokacin da ake ba su kulawar gaggawa

Kakakin 'yan sanda a jihar ta Kaduna, Muhammad Jalige ya tabbatar wa BBC da kai harin, amma bai yi karin haske kan adadin mutane da aka kashe ba.

Sai dai yana mai cewa hukumomi na tattara bayanai, ya kuma kara da cewa suna iya kokarinsu don tabbatar da tsaro a jihar.

An sha kai irin wannan muggan hare-hare a kan babura a jihohi da dama da ke arewa maso yammacin Najeriya, tare da kashe ko sace mutane don neman kudin fansa wani lokaci a kwashe musu dukiyoyi.

A ranar Asabar ma, an kashe akalla jami'an tsaro 16 ciki har da manyan hafsoshi uku yayin da suka yi kokarin kutsawa cikin wani daji da 'yan fashi ke mafaka a jihar Katsina.

Sojojin Najeriya sun ce sun yi nasarar kashe mutum 17 daga cikin 'yan fashin a lokacin musayar wuta.

Sama da mutum dubu takwas ne suka rasa rayukansu sakamakon irin wadanan hare-hare a cikin shekaru 10 a yankin arewa mao yammacin Najeriya.

Source: BBCHAUSA

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "'Yan bindiga sun kashe mutum 18 a gidan biki a Kaduna"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?