--
Yadda sharhi a Facebook ya kashe aure, bayan amarya ta ce za ta ci amanar angonta idan aka bata N200k

Yadda sharhi a Facebook ya kashe aure, bayan amarya ta ce za ta ci amanar angonta idan aka bata N200k




Wata mai amfani da shafin sadarwa na Twitter, mai suna Gospel Josiah, ta bar mutane cikin mamaki bayan ta wallafa wani labari na wata mata da aurenta ya mutu sakamakon sharhi da tayi a wani rubutu da aka wallafa a Facebook din.

A yadda matar ta rubuta, an wallafa wata tambaya ne a shafin na Facebook, inda ake tambayar mutane su bayyana ra’ayinsu akan za su iya cin amanar abokanan aurensu akan naira miliyan 10? Matar wacce bata jima da yin aure ba ta yi sharhi akan wannan rubutu.

Matar ta ce miliyan 10 yayi yawa, inda ta ce za ta ci amanar mijinta akan kudin da bai kai wannan yawa ba. Ta rubuta cewa za ta ci amanar mijinta akan naira dubu dari biyu kacal.

“Ta ce wannan kudin ya yi yawa, za ta ci amanar mijinta idan aka ba ta naira dubu dari biyu kacal. Wani wanda ya santa ya sanar da ita akan ta goge wannan rubutu, saboda bata jima da yin aure ba.”

A cewar labarin, mutane biyu sun kara yi mata magana akan ta goge wannan rubutu, amma sai ta mayar musu amsa da cewa: “Auren waye? Babu abinda za a gani a gabana koda nayi.”


Daga baya ta goge wannan sharhi da tayi, sai dai kuma ta riga ta makaro, domin kuwa wasu daga cikin dangin mijin sun riga sun dauki hoton wannan sharhi da tayi suka turawa surukarta, wacce take babbar ma’aikaciya ce.

Wannan ya kawo matsala sosai, hakan ya sanya aka gabatar da taro don shawo kan wannan matsala. An kira amaryar inda ta zo tana hawaye, ta ce ita da wasa take yi, amma ina kowa yaki yadda da ita.

A cewar Gospel tuni aka raba auren, inda iyayen angon suka ce za su je su karbo kayan aure da sadaki da suka kai.




SOURCE:PRESSLIVES.COM

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Yadda sharhi a Facebook ya kashe aure, bayan amarya ta ce za ta ci amanar angonta idan aka bata N200k"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?