Yadda dan sanda ya dinga lalata da ni tun dare har asuba - Matar da ta take doka
Friday, 31 July 2020
Comment
Wani lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Prince Wiro, ya yi kira ga rundunar 'yan sandan jihar Ribas da ta zakulo wasu 'yan sanda da wata mata mai takaba ke zarginsa da yi mata fyade saboda take dokar covid-19 da tayi.
Matar mai takaba mai shekaru 32 ta zargi wani dan sanda da ke aiki da ofishin Sakpenwa, karamar hukumar Tai, da saceta a ranar Talata inda ya kai ta masaukinsa sannan ya dinga yi mata fyade bayan tsorata ta da yayi da bindiga.
Tace: "Ina komawa gida daga Bori a Fatakwal lokacin da na hadu da dan sandan a kan titi. Sun tsareni saboda ban saka takunkumin fuska ba. Sun tsareni na dogon lokaci.
"Bayan nan, sun kai ni wani wuri inda suka ce za su wuce da ni ofishinsu amma basu kaini ba. "Bayan wani lokaci, sun kaini masaukinsu inda daya daga cikinsu ya dinga yi min fyade har asuba."
Ayayin martani a kan abinda ya faru, Wiro, ya bukaci rundunar 'yan sandan da ta fara bincike a kan wannan zargin. Ya ce: "Babu adalci a kan yi wa mace fyade saboda ta take dokar jihar Ribas na kin amfani da takunkumin. Ina tsammanin 'yan sandan za su yi wani abu a kai.
"Kun san akwai wani umarni da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya bada na yin duk abinda ya dace wurin kawo karshen fyade." Wacce abun ya faru da ita ta sanar da aukuwar lamarin tun bayan da aka kai ta gidan.
"An kaini masaukin baki a kan takunkumin fuska na N100. "Abun da bada mamaki. Yana son yin lalata da ni. Zai kashe ni. Ya hana ni daukar waya kuma yana barazanar kwace wayata," ta tura a matsayin sakon kar ta kwana.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ya ce ana duba lamarin. Ya ce matar ta kai rubutaccen bayani a kan abinda ya faru. Ya ce: "ana duba lamarin a halin yanzu. Ana kokarin gano 'yan sandan da suka aikata abinda ake zargin kuma za a dauka mataki."
SOURCE: LEGIT.NG
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Yadda dan sanda ya dinga lalata da ni tun dare har asuba - Matar da ta take doka"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?