
Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa
Thursday, 16 July 2020
Comment
![]() |
Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa. Hoto daga TVC Source: Twitter |
Idan za mu tuna, ana bincikar pondei ne a kan wasu miliyan N40 da suka yi batan dabo a hukumar, ya fice daga majalisar a ranar Alhamis yayin da ake bukatar jin ta bakinsa. Shugaban NDDC ya zargi shugaban kwamitin majalisar wakilan masu alhakin bincikarsu, Olubunmi Tunji-Ojo, da rashawa.
![]() |
Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa. Hoto daga TVC Source: Twitter |
A yayin jawabi ga kwamitin, Pondei ya ce, "Mu a NDDC ba mu amince da shugaban kwamitin binciken nan ba. "Ana zarginsa da saka siyasa a al'amuransa. Yana saka siyasa kuma mun tabbatar da cewa ba za a mana adalci ba."
"Ba mu da matsala a kan bayanin da aka bukace mu mu yi da kuma bayyana gaban kwamitin wucin gadin. Amma matukar yana nan, babu wani bayani da za mu yi," yace.
A wani labari na daban, jami'an 'yan sandan Najeriya sun tsinkayi gidan Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktan hukumar habaka yankin Neja Delta (NDDC), inda suka yi masa zobe.
![]() |
Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa. Hoto daga TVC Source: Twitter |
Jami'an tsaron sun isa gidan ne da ke lamba 3, titin Owuru Creek, kusa da titin Herbert Macauley da ke tsohuwar GRA a Fatakwal, jihar Ribas a sa'o;in farko na ranar Alhamis. Wannan ci gaba ya faru ne kafin isar Nunieh gaban kwamitin bincike na majalisar dattawa da ke Abuja inda za ta amsa tambayoyi a kan ayyukan NDDC.
A yayin da jaridar The Cable ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, Omoni Nnamdi don tsokaci,
ya bukaci a kira sa nan da mintuna 30. Akpabio da Nunieh sun bayyana a gaban kwamitin rikon kwarya na majalisar dattawa, inda ake bincikarsa a kan badakalar wasu kudade har N40 biliyan wanda kwamitin rikon kwarya na hukumar suka lamushe. A yayin sauraronsu, Akpabio ya ce bai san tsarin kudin kashewa na NDDC ba karkashin Nunieh saboda bata bashi bayanin da ya kamata.
SOURCE: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?