
Wata sabuwa: Na'abba, Shehu Sani da wasu 'yan gwagwarmaya 28 za su kirkiri sabuwar jam'iyya
Wednesday, 1 July 2020
Comment
![]() |
Ghali Na'abba, Oby Ezekwesili, Femi Falana da Shehu Sani Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Punch |
Akidar wannan sabuwar tafiya ta siyasa, ba ta wuce hada kan 'yan Najeriya domin yi sauya fasalin kundin tsarin siyasa da kuma shimfidar wata sabuwar hanyar samar da sabon tsari na jagoranci.
Wannan yana ƙunshe cikin wata sanarwa da ta fitar bayan doguwar tattaunawa ta tsawon watanni da kuma taruka daban-daban da rika gudanarwa.
Daga cikin jerin kwamitin mutum 30 na 'yan gwagwarmayar da za su jagoranci wannan sabuwar tafiya ta siyasa, sun hadar da tsohon kakakin majalisar wakilai; Ghali Na'abba, tsohon mataimakin babban bankin Najeriya; Dr. Obadiah Mailafia.
Sauran sun hadar da; Olisa Agbkoba, Femi Falana, Kanal Abubakar Umar mai ritaya, Dakta Oby Ezekwesili, Farfesa Jibo Ibrahim, Yabagi Sanni; Ambasada Nkoyo Toyo, Isa Aremu, Farfesa Chidi Odinkalu, da Sanata Shehu Sani.
Ragowar 'yan kwamitin sun hada da; Farfesa Remi Sonaiya, Mallam Tanko Yunusa, Alhaji Shettima Yerima, Lady Funke Awolowo, Peter Ameh, Ogbeni Manre Banjo da sauransu.
Kungiyar za ta fito fili ta bayyana kanta a wannan wata na Yuli.
Daga cikin shawarwarin da kungiyar ta yanke sun hadar da neman magoya baya daga duk wani kwararo da sako na kasar masu akidar kawo sabbin sauye-sauye a tsarin siyasa da jagoranci domin ci gaban kasa.
Haka kuma, kungiyar za ta mayar da hankali wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaba al'umma da aminci a tsakaninsu kamar yadda babi na biyi a kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadi.
Mambobin kungiyar sun kuma bayyana takaicinsu dangane da yadda gwamnatin kasar ta gaza bai wa al'umma kariya daga ta'addancin 'yan fashin da makami, 'yan daban daji da sauran masu tayar da kayar baya.
Sun kuma ce lokaci ya yi da ya kamata ‘yan Nijeriya su tashi su farga tare da yiwa kawunansu kartun ta nutsu wajen ceto kasar daga durkushewa sakamakon rashin shugabanci na gari.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Wata sabuwa: Na'abba, Shehu Sani da wasu 'yan gwagwarmaya 28 za su kirkiri sabuwar jam'iyya"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?