--
Wata sabuwa: hand 'sanitizer' ta kashe mutum 9 a Indiya

Wata sabuwa: hand 'sanitizer' ta kashe mutum 9 a Indiya



Akalla mutum tara suka mutu a Indiya bayan sun sha man wanke hannu wanda ake kira sanitiza mai ɗauke da sinadarin sa maye.

Siddharth Kausal, wani babban ɗan sanda a ƙauyen Kurichedu da ke Indiya ya shaida cewa mutane da dama shan giya ya zama musu jiki ko kuma tamkar jaraba a gurinsu wanda hakan ya ja suke shan man wanke hannu sakamakon yana ɗauke da sinadarin saka maye wanda ake kira Alcohol.

"Babu wadataciyyar giya a shaguna sakamakon dokar kulle, amma ba wuya ake samun man wanke hannu," in ji shi.

Ya ƙara da cewa wasu mutanen da suka sha man wanke hannun ba su mutu ba suna asibiti, wasu kuma an sallame su.

A halin yanzu dai an fara bincike kan mutuwar waɗanda suka sha wannan mai.
Lamarin dai za a iya cewa ya faru ne yayin da yawan waɗanda suka mutu sakamakon korona a Indiya ya zarce mutum 35,000 a ranar Juma'a.

Yanzu dai sama da mutum miliyan 1.6 ne suka kamu da cutar korona a Indiya.

Indiya ce ta uku a yawan masu vutar bayan Amurka da Brazil da ke kan gaba.

SOURCE: bbchausa/

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Wata sabuwa: hand 'sanitizer' ta kashe mutum 9 a Indiya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?