
Umar Yusuf: Matashi a Borno ya kera kekunan da za su tallafawa jama’a
Wednesday, 8 July 2020
Comment
Umar Yusuf, wani Matashi daga jihar Borno ya na abin a gani - a yaba - Yusuf ya na kera kekuna masu kyau duk da cewa bai da isassun kayan aiki Idan da Gwamnati za ta taimakawa wannan Bawan Allah, da ya yi fice
Wani Matashi mai suna Umar Yusuf ya nunawa Duniya cewa akwai masu basira a Arewacin Najeriya, inda ya hada wasu kekuna masu ban-kwaye. Mutane sun fara kira ga gwamnati da hukumomin da ke da alhakin taimakawa wannan matashi wajen cin ma burinsa.
Idan gwamnati ta tallafawa Umar Yusuf, hakan zai zaburar da ire-irensa wajen bayyanawa Duniya basirarsu. Duk da cewa Yusuf bai da wasu kayan aiki, ya na amfani da hannuwansa wajen kera wadannan kekune wadanda idan aka samu irinsu da yawa za su taimakawa kasar.
Daga cikin hanyar da wadannan kekuna na gida za su taimakawa Najeriya akwai samar da ayyukan yi, da kuma rage kashe kudi wajen shigo da kaya daga ketare.
Wannan matashi mai basira ya na zaune ne a garin Maiduguri, babban jihar Borno a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. Ba kasafai aka saba jin labarin masu baiwa irinsa ba. Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar North East Reporters,
Umar Yusuf ya hada irin wadannan kekuna rututu a Maidguri, kuma a shirya ya ke da ya kara hada wasu. Shagon da matashin ya ke aiki ya na kan titin Gomborun-Ngala a kusa da wani asibitin ‘yan sanda da ke Maiduguri. Wani Kabir Ajibola ya fito ya na rokon gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya taimakawa Yusuf da tallafi yadda zai bunkasa. Shi ma
Abdulhamid Abubakar Girei ya yi irin wannan kira, ya ce a hada Matashin da manyan gwamnatin jihar Borno domin su ga irin rawar da ‘dan kasar su ya ke takawa.
SOURCE: LEGIT.NG
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Umar Yusuf: Matashi a Borno ya kera kekunan da za su tallafawa jama’a "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?