--
Tirkashi: Yadda na gano cewa ina da ciki a ranar dana haihu – Budurwa ta bayyana hakan

Tirkashi: Yadda na gano cewa ina da ciki a ranar dana haihu – Budurwa ta bayyana hakan


Wata budurwa ta bayyana yadda ta gano cewa tana dauke da ciki a ranar da ta haifi jaririnta.

Ta ce:

“Na gano cewa ina da ciki a ranar dana haihu. Dana sunan shi Smangaliso, ni da mahaifiyata muna goge-goge kawai sai naji wani ciwo mai tsanani ya dameni, na yi tunanin ko lokacin al’adata ne yayi, amma ina ciwon ya cigaba.

“Mahaifiyata ta kira fasto saboda ita ma abin yafi karfinta. Faston ta zo gidanmu ta ce za ta yi mini addu’a, haka muka cinye daren baki daya muna addu’a.

“Tsabar ciwo ya kai ga idan ina yin kukan ma hawayen baya fitowa. Da misalin karfe 1 na dare sai na fara jin kamar wani abu yana shirin fitowa daga cikina. Faston ta ce mini na shiga bandaki. Abinda ta ce mini shine zamu kawo karshen wannan shaidanin yau.

“A lokacin da muka shiga bandakin, ta gano cewa ina nakuda ne a wannan lokacin.

“Cikin gaggawa ta nemi a bata reza ta fara tayani domin na samu na haihu. A lokacin da ta samu ta karbi jaririn ni kuma na riga ma suma a lokacin, mahaifiyata ta fito daga gida da gudu a lokacin da ta fara jin kukan jariri.

“Cikin gaggawa muka garzaya zuwa asibiti cikin jini, tare da jaririn a cikin tawul. Bayan zuwan mu suka duba mu suka tsabtace jaririn suka sanya masa kaya masu kyau.“






 SOURCE: PRESSLIVES.COM

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Tirkashi: Yadda na gano cewa ina da ciki a ranar dana haihu – Budurwa ta bayyana hakan"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?