--
Tirkashi: Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi

Tirkashi: Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi




Rundunar 'Yan sandan Jihar Niger ta ce ta kama wani Sani Garba mai shekaru 32 a kan yi wa wata dattijuwa mai shekara 60 fyade.

A cewar jaridar Punch, Garba da rundunar 'yan sandan ta yi holensa a ranar Juma'a ya ce mazaunin gyatumai ke ne ke jan hankalinsa da tayar masa da sha'awa. Wanda ake zargin ya kuma ce yana jin dadin lalata da mata masu shekaru da yawa a unguwarsu saboda ba shi da kudin neman budurwa.

Ya kara da cewa ya yi wa fiye mata masu shekaru da yawa fiye da uku fyade a unguwarsu, ya ce ya yi nadamar aikata abinda ya kira “shirme”. "Tunda ba ni da kudin rike budurwa. Na gwammace in rika lalata da tsofafin mata a unguwar mu kuma ina jin dadin hakan. "Wasu lokuta na kan tambayi kai na me yasa na ke aikata wannan shirmen?’

Na yi takaicin tsintar kaina a wannan halin," in ji shi. Wasiu Abiodun,Kakakin rundunar, ya ce jami'an hukumar na 'B' Division ne suka kama wanda ake zargin a Suleja da ke jihar. Abiodun ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.

An ce wanda ake zargin ya yi kuste gidan wata mata mai yawan shekaru a ranar 18 ga watan Yuli misalin karfe 4:30 na yamma kuma ya yi mata fyade. Hakan na zuwa ne bayan yawaitan fyade da ake samu a sassan Najeriya daban daban.

A wani rahoton, kunji wasu 'yan bindiga sun sace dan sanda mai mukamin sufeta, matan wasu fitaccen mafarauci da wasu mutane biyu a garin Koma da ke jihar Adamawa kamar yadda The Nation ta ruwaito. 'Yan bindigan sun sace mutane shidan ne daga gidajensu da tsakar dare a garin na Koma da ke karamar hukumar Jada ta jihar Adamawa.

Majiyarmu ta gano cewa maharan a safiyar ranar Alhamis sun kashe mutum daya da ake tunanin ya zame barazana gare su. Rahotanni sun ce yan bindigan masu yawa sun shiga garin na Koma sannan suka fara bi gidajen wadanda suke son sacewa daya bayan daya suna daukan su.

SOURCE: LEGIT.NG

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Tirkashi: Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?