
Tashin hankali: Obasanjo ya yiwa wata mata dukan tsiya da dorina akan ta sace mishi naira miliyan 160
Thursday, 23 July 2020
Comment
Mutanen Olaogun dake yankin Ifo Ibogun cikin jihar Ogun sun tashi cikin mamaki a ranar Talata, a lokacin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya shiga yankin da mota cike da jami’an tsaro, inda suka yiwa matar dan uwansa na jini Adebayo Molaja duka, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.
An ruwaito cewa Obasanjo da kanshi yayi amfani da bulala ya zane Mrs Adebayo akan zarginta da ake da sace naira miliyan 160.
Ba a tabbatar da yadda lamarin ya samo asali ba, da kuma abinda ya tunzura tsohon shugaban kasar ba, wanda yake kuma tsohon soja ya dauki wannan mataki.
Ba a tabbatar da yadda lamarin ya samo asali ba, da kuma abinda ya tunzura tsohon shugaban kasar ba, wanda yake kuma tsohon soja ya dauki wannan mataki.
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a boye sunanshi saboda wani dalili, ya sanar da Sahara Reporters cewa an jiyo Obasanjo yana dakawa mata tsawa yana ce mata “Omolaja, Ole! Abiodun Ole! Won Loji N160m (Omolaja barawo! Abiodun barawo! sun ce kin saci N160m)” a lokacin wannan lamari.
Mutumin ya kara da cewa, “Obasanjo ya fito daga gonarshi da misalin karfe 5:00 na safe a lokacin da mutane suke bacci. Wasu jami’an tsaro ne suka rako shi zuwa gidan na Adebayo.
“Yana zuwa ya fara kwalawa Mrs Adebayo kira, ya sanya jami’an tsaron suka zagaye wajen. Daga nan sai ya fara dukanta da bulalar.
“Mutane da yawa na yankin sun yi mamaki sosai. Daruruwan ‘yan acaba da suka zo wucewa sun tsaya a wajen don bawa idonsu abinci, inda suke mamakin shin fashi da makami ne aka yi ko kuwa.”
SOURCE: PRESSLIVES.COM
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Tashin hankali: Obasanjo ya yiwa wata mata dukan tsiya da dorina akan ta sace mishi naira miliyan 160"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?