
Tashin hankali: Matashi yayi barazanar saka bam a dakin majalisar tarayya da kamfanin NNPC idan ba a bashi kayan tallafi ba
Friday, 24 July 2020
Comment
An yankewa wani matashin saurayi da yayi barazanar saka bam a helkwatar kamfanin man fetur na kasa (NNPC), akan kayan tallafin cutar COVID-19, hukuncin shekara biyu a gidan yari.
Wata kotun Majistire dake zaune a Lokoja, babban birnin jihar Kogi, ta yanke hukuncin amma ta bayar da damar beli ga mai laifin.
Matashin mai suna Adeoye, mai shekaru 35 da ya fito daga karamar hukumar Okehi cikin jihar Kogi, ya amsa laifinsa akan abinda ake zargin shi da shi, bayan jami’an hukumar DSS sun gurfanar da shi a gaban kotun wacce mai Shari’a A.S. Ibrahim yake jagoranta.
Jami’in DSS din da ya gurfanar da shi mai suna O.A Yahaya, ya ce saurayin ya yiwa kwamitin gudanarwa akan cutar COVID-19 barazana, inda ya bukaci kayan tallafi ko kuma ya sanya bam a dakin majalisa da kuma NNPC.
Bayan ya roki ayi masa sassauci, matashin da yake dalibi ne, kuma shi daya ne a wajen mahaifinsa, kuma yayi alkawarin ba zai kara ba, alkalin ya yanke masa hukuncin shekara biyu a gidan yari.
Sai dai kuma, jami’in DSS din ya ce suna cigaba da duba akan wannan hukunci da alkalin ya yanke domin kuwa suna ganin kamar yayi sauki da yawa.
SOURCE: PRESSLIVES.COM
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Tashin hankali: Matashi yayi barazanar saka bam a dakin majalisar tarayya da kamfanin NNPC idan ba a bashi kayan tallafi ba"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?