--
Tashin hankali: Ma’aurata sun samu nasara a kotu, za su sanyawa dansu suna ‘Shaidan’

Tashin hankali: Ma’aurata sun samu nasara a kotu, za su sanyawa dansu suna ‘Shaidan’


Wasu ma’aurata daga kasar New Zealand, sun samu nasara a kotu, inda za su sanyawa dansu dan wata hudu a duniya suna ‘Shaidan’, bayan mai rijistar suna yayi kokarin hana su sanyawa dansu sunan.

Dan, wanda yake shine shugaban wani kamfani dake Derbyshire, ya kai korafi akan yadda aka yi musu shida matarsa a lokacin da suka je yiwa dan nasu rijistar suna a ofishin da ake yi bayan shafe watanni a kulle saboda annobar coronavirus.

Ya ce: “Mun je ofishin cikin farin ciki domin yi masa rijista, amma matar sai ta kalle mu cikin rainin hankali.

“Ta ce mana ba zai taba samun aiki ba, sannan kuma malaman makaranta baza su koyar da shi ba.

“Nayi kokarin yi mata bayani cewa mu bamu da addini, amma taki sauraron mu.

“Ta gaya mana cewa sabawa doka ne ma a kasar New Zealand a sanyawa yaro irin wannan suna.“

Bayan sun takura akan sai an sanyawa dan nasu wannan suna, matar ta bukaci su fita daga ofishin za ta duba idan za ta iya sanyawa dan nasu sunan Shaidan.

Dan ya kara da cewa: ‘Bamu ji dadin abinda tayi mana ba.

‘Mu a wurin mu suna ne mai dadi, kuma suna ne na daban. Bamu sanya masa don samun bacin rai ba.

Kasar New Zealand da take da mataki mai tsauri akan sunayen mutane, ta sanya sunan Lucifer wato Shaidan a cikin jerin sunayen da ta haramta a shekarar 2013, bayan shi ta hana sanya suna ‘Christ’ da kuma sunayen sarauta irinsu ‘King’, ‘Prince’, da ‘Princess’. Mai magana da yawun gwamnatin Derbyshire, ya ce matar tayi daidai da taki yadda ta sanya sunan.

Mai magana da yawun ya ce:

“Duk da shawarar da aka basu, ma’auratan sun takura akan sanyawa dan nasu wannan suna, hakan ya sanya tayi masa rijista da wannan suna.

“Muna basu hakuri idan hakan bai yi musu dadi ba, amma aikin rijistarar mu ne hakan ta bawa mutane shawara, saboda a lokuta da dama mutane basu san ainahin abinda wasu sunayen ke nufi ba.“

SOURCE: PRESSLIVES.COM

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Tashin hankali: Ma’aurata sun samu nasara a kotu, za su sanyawa dansu suna ‘Shaidan’"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?