Shugaban kugiyar izalah reshen jos yayi muhimmin kira akan bude makarantu
Sunday, 12 July 2020
Comment
Shugaban majalisar malamai ta kasa na kungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga gwamantin tarayya da na jahohi da su bude makarantu don a cigaba da koyo da koyarwa a ciki.
Sheikh Sani Jingir ya kara da cewa ko kasar Sin da Amurka da suke da anmobar sun bude makarantu ana ci gabada koyarwa. Amma a Nijeriya da ba annobar an rufe yara a gida an hana su zuwa makaranta.
Sheikh Sani ya ci gaba da cewa akwai wasu masu mugun nufi ga 'yan Nijeriya a cikin mukarraban Gwamnatin Buhari. Ya ce an yi kitso da kwarkwarta, inda ya yi kira ga Buhari da ya yi garambawul a Gwamnatinsa ya cire miyagu a cikin ma'aikatu.
Sheikh Jingir ya yi wanan jawabin ne a yayin da yake gabatar da nasihar Juma'a a masallacin Juma'a na 'yan Taya dake birnin Jos.
A karshe Sheikh Jingir ya yi addu'a ga shugaban 'kasa Muhmmadu Buhari da Gwabnan jahar Filato Simon Bako Lalong.
SOURCE: SHAFIN RARIYA NA FACRBOOK
Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Shugaban kugiyar izalah reshen jos yayi muhimmin kira akan bude makarantu"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?