--
Shiga Jamhuriyar nijar ta barauniyar hanya yasanya An daure ‘yan Najeriya da aka maido daga Nijar

Shiga Jamhuriyar nijar ta barauniyar hanya yasanya An daure ‘yan Najeriya da aka maido daga Nijar



Babbar Kotun Tarayya ta Katsina ta daure wasu ‘yan Najeriya watanni uku-uku a saboda laifin shiga Jamhuriyar Nijar ba bisa ka’ida ba.

Hukumar shige da fice ta Najeriya ta gurfanar da mutanen su 12 ne bayan sun tsallake iyakar Jamhuriyar Nijar ta barauniyar hanya amma aka kama su aka dawo da su Najeriya.

Da take yanke hukumci bayan masu laifin su amsa laifukansu, Mai Shari’a Hadiza Shagari ta ba kowanensu zabin biyan tarar Naira dubu hamsin ko zaman kurkuku na wata uku.

Lauyoyin masu laifin da masu gabatar da kara, Barista Najib Abdullahi da Barista Obilor Collins duk sun aminta da hukuncin kotun.
Aminiya ta ruwaito cewar wadanda aka yanke wa hukumci ‘yan asalin jihohin Inugu da Edo da Legas da Ribas da Ogun da Delta da kuma Abiya ne.

Suna kuma daga ciki mutum 42 da aka maido Najeriya ta iyakar Jamhuriyar Nijar da ke Kongolam.

Za kuma a gurfanar da sauran mutum 30 a gaban kuliya idan aka gama tantance su.

SOURCE: https://aminiya.dailytrust.com.ng/


TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Shiga Jamhuriyar nijar ta barauniyar hanya yasanya An daure ‘yan Najeriya da aka maido daga Nijar"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?