
Sharaɗi biyar da dokar hana yabon Annabi a Kano ta ƙunsa
Thursday, 9 July 2020
Comment
Gwamnatin jihar Kano ta ce babu wani sha'iri da zai ƙara waƙar begen Annabi a jihar sai idan ta ba shi lasisi.
Ta ce riƙon sakainar kashi da ta ga mawaƙan na yi da damar da aka ba su ne ya sa ta fito da waɗannan sabbin sauye-sauye.
Shugaban hukumar Isma'il Muhammad Na'abba wanda aka fi sani da Afakallah a wata hira da BBC ya ce, ƙimar da ake ganin sha'irai ke da ita a baya ce take neman zubewa, abin da su kuma ba za su bari ba.
Ya sha alwashin cewa duk mutumin da aka kama da irin waƙoƙin da ke taɓa matsayin fiyayyen halitta ko kuma wani mai daraja ko Ubangiji da kansa ba za su bari ba sai sun ɗauki mataki.
Ga wasu daga cikin sharuɗɗan da dokar ta kunsa:
Babu wani mawaƙi da zai ƙara waƙa sai da shaidar lasisin da gwamnati ta ba shi.
Ko da mawaƙi na da lasisin izini to sai ya kawo waƙar ta shi an saurara idan da wani abu da ya ci karo da dokar hukumar a cire shi.
An haramta majalisi a jihar sai da izini daga hukumar, kuma ko da izini an daina yi a cikin wuraren zaman jama'a ko kusa da masallaci ko kuma kusa da kasuwa.
Babu makarantun Islamiyya cikin wannan mataki, saboda suna samun kulawa kai tsaye daga gwamnati ta wasu hanyoyin.
Ba za a yarda da ana majalisi ana haɗa mata da maza ba ko kuma mawaƙi ya riƙa rawar shoki ko kuma wani abu makamancin haka.
Afakallah ya ce waɗanda kawai suka yi rijista da hukumarsu ne za su ci gaba da waƙoƙin bege a fadin jihar.
Ya kuma ce "Tuni muka nemi gidajen rediyo a Kano su daina sanya irin waɗannan waƙoƙi har sai lokacin da muka bayar da izini".
SOURCE: BBCHAUSA
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Sharaɗi biyar da dokar hana yabon Annabi a Kano ta ƙunsa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?