Sau 6 kacal na taba lalata da yarinyar, mahaifiyarta ce ke zuzutawa - Wanda ake zargi
Thursday, 16 July 2020
Comment
Wani mutum mai shekaru 40 mai suna Edet Imoh, ya amsa laifin da ake zarginsa a gaban 'yan sandan jihar Legas. Ya tabbatar da cewa yayi lalata da diyar makwabcinsa mai shekaru 11 "amma sau shida kacal ba kamar yadda mahaifiyar yarinyar ke cewa da yawa ba".
'Yan sanda sun kama Imoh wanda ke zaune a titi daya da mahaifan yarinyar a titin Oyekanle da ke Bariga da ke tsakiyar birnin Legas, bayan rahoton da mahaifiyar yarinyar ta kai wa ofishin 'yan sanda da ke Bariga a ranar 25 ga watan Yunin 2020.
An zargi cewa, a duk lokacin da wanda ake zargin ke son lalata da yarinyar, zai kirata dakinsa a kan cewa zai aiketa siyo wani abu. Asiri ya tonu bayan da wani makwabcinsu ya lura da hakan tare da sanar da mahaifiyar yarinyar yayin da take neman diyarta.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya ce "an kama wanda ake zargi wando a kasa yayin da karamar yarinyar ke kwance yana lalata da ita. "A yayin da aka tambayeshi yayi bayanin abinda ya faru sai yace aikin shaidan ne. Ya ce sau shida kacal ya taba lalata da yarinyar ba sau da yawa ba da mahaifiyarta ke ikirari."
A wani labari na daban, yarinya mai shekaru 14 mai suna Anita Haledu Ibrahim ta kashe kanta bayan cikin shege da ta dauko. Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Anita daliba ce a makarantar gwamnati ta kimiyya da ke Andaha kusa da Akwanga. Ta sha maganin kwari don kashe kanta a ranar Asabar, 11 ga watan Yulin 2020.
Kamar yadda majiyoyi suka sanar, saurayin Anita ya dirka mata ciki bayan haduwarsu a Andaha yayin kullen korona. Sun shaku har ta samu ciki amma daga baya sai ta koma kauyensu da ke Abuja. Bayan iyayenta sun tuntubeshi, ya amsa cikin kuma ya bayyana bukatar aurenta.
Anita ta yanke hukuncin kashe kanta bayan mahaifinta, Haledu Ibrahim, ya yi mata mugun duka a kan cikin. Ta sha maganin kwarin a ranar Asabar, 11 ga watan Yuli amma an gaggauta kai ta asibiti inda ta cika a ranar 14 ga watan Yuli. 'Yan uwanta na shirye-shiryen birneta.
SOURCE: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Sau 6 kacal na taba lalata da yarinyar, mahaifiyarta ce ke zuzutawa - Wanda ake zargi "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?